Monday, April 9, 2007

[kanoshia] FREEDOM REDIYO TSUNTSUN DA YA JA RUWA............


Edita, amincin Allah ya kara tabbata ga iyalan Manzon Allah (SAW) da masoyansu. Bayan haka ina rokon ka da kabani fili a wannnan jarida tamu ta masoya gidan Manzon Rahama (SAW) domin in yi tsokaci akan wani abu da ya faru a jihar Masoya Manzon Rahama (SAW) jihar da ta fi kowace jiha a duniyar bakaken fata yawan Masoya Manzon Rahama (SAW) da iyalansa tsarkaka, wannan jiha itace jihar Kano. A ranar Talata 15 ga watan Rabi'ul Awwal ina zaune a gida ina saurararen labaran Inda ranka da rediyon Freedom yake gabatarwa sai naji mai gabatar da shirin yana cewa wasu 'yan ta'adda sun kaiwa wannan gidan rediyo da yake yiwa aikin kodago ya samu na kalaci hari. Wannan labari ya bani mamaki ganin ruwa baya tsami banza sai na saurari mai kawo labarin ko naji dalilin haka amma har ya kare gabatar da shirin ban ji musabbabin wannnan al'amari ba. Wannan abu ya tsaya mini a rai a saboda haka da safe sai nayi tambaya ga jama'ar gari inda suka fada mini ai wannan gidan rediyo shine ya jawo kansa abin daya faru dashi domin sun yi wani shiri akan Mauludin Manzon Rahama (SAW) inda suka ki rawo wani mutum domin ya soki maulidin Manzon Rahama (SAW) inda shi wannnan mutumi wanda wannan gidan rediyo ya kirawo Dan izala ne wanda shi a nasa irin illimin Mauludin Manzon Rahama (SAW) haramun ne, inda yayi amfani da wannan dama wajen sukar Mauludin Manzon Rahama (SAW)  wanda sai faduwa tayi daidai da zama domin shi kansa mai gabatar da shirin makiyin Maulidin Manzon Rahama (SAW) ne, kuma makiyinmu masu bin darikun sufaye da 'yan uwanmu shi'a domin da kunne na nasha sauraran irin shirye shiryen da wannan mutumi yake gabatarwa shi mai shugabantar bangaren addinin na wannan tasha ta Freedom inda a kullum baya boye gabarsa a garemu mu 'yan darika da kuma 'yan uwanmu shi'a duk kuwa da kasancewar aikin jarida yake yi wannan aka koyar dashi daidaita gaskiya ba tare da marawa wani bangare baya ba amma wannan mutumi a kullum bashi da aikin da yake yi sai neman cin fuskar mu 'yan darika da 'yan uwanmu shi'a domin a zahiri yake nuna kiyayyarsa ga gidan Manzon Allah (SAW) da masu kaunar Sayyada Fadima (AS) domin bana mancewa da wata rana da yayi hira da Marigayi Sarkin Yakin Waliyyan Allah Sheik Umar Ta'ambo wanda a cikin hirar yayi ta kokarin ya sanya Malamin yayi suka ko ya fadi wata kalma muguwa ga 'yan uwanmu 'yan shi'a amma da yake Malamin Masoyi ne na gidan Manzon Allah (SAW) sai ya kaucewa wannan sharri. Duk irin kalmomin da wancan mutumi yake fada akanmu mu 'yan darikun sufaye muna sane da shi kuma muna ji da kunnuwanmu amma mun san makircin bil adama ba mai zuwa ko ina bane ba.
Idan na dawo magana akan wani shiri da wannan gidan rediyo yake gabatarwa a duk ranakun Jumma'a inda Malamina wanda ya koyar dani falalar salatin Manzon Allah (SAW) a makaranta tun ina karamin yaro yake gabatarwa wato Marigayi Mallam Ahmad Koki, wannan shiri sunansa Muharraka, wannan shiri ne da ake kirawo mawakan Manzon Allah (SAW) inda suke kara mana soyayyar Manzon Rahama (SAW) amma sai ga shi daga barin duniyar mai gabatar da shirin wannan mutumi dan Izala na rediyo Freedom ya dauki hanyar salwantar da wannan shiri ta hanyar kin barin Malam Nasiru Abdulhamid Dantata da Malam Ya'u Dodo su cigaba da gabatar da wannan shiri na Muharraka wanda suka saba gabatarwa su da Marigayi Malam Ahmad Koki, inda shi wancan Mutumi ya nemo wani wanda kwata kwata bai cancanci a bashi damar cigaba da shirin ba, yayi haka ne kuwa saboda ganin shirin ba kowa yake farantawa rai ba sai 'yan darika masoya Manzon Allah (SAW) da Iyalansa tsarkaka.
Freedom rediyo zan yi kira ga darektocin wannan gidan rediyo da su sani fa mu musulmi masoya Iyalan gidan Manzon Allah (SAW) wadanda muka yi imani da kalmar shahada daya tana maida kafirn da ya shekara dari cikin tsafi da kafirci musulmi kuma muke bin 'yan uwa musulmi sallah ba tare da mun raba masallatanmu kuma muke raya daren da aka haifi fiyayyen halitta (SAW) da karatun alkur'ani da yabonsa (SAW) mune kaso casa'in na musulmin jihar Kano, don haka zai yi kyau wannan hukumar gidan rediyo tayi sauye sauye a bangaren addinin musuluncinta domin sanya kwararrun ma'aikata 'yan jarida masu mutunci masu tsayawa a iya aikin jaridarsu ba tare da nuna bangaren da suke ba domin ko yaro karami yasan bangaren addinin gidan rediyon freedom mai shugabantar wannan bangare shine ya jawowa wannan gidan rediyo wanda dukkan dan halas din Kano yake alfahari da shi asarar da wannan gidan rediyo yayi domin irin kalmomin da yake amfani dasu sun sabawa kalmomin da dan jarida da ya shiga ajin koyar da aikin jarida ya dace yayi amfani dasu ba.
Ina kuma kira da jama'a yan uwana mabiya darikun sufaye da mu fahimci cewa wannan gidan rediyo na freedom ya bamu dama mai tarin yawa wajen sanya abubuwan da suke kara mana shaukin soyayyar Manzon Rahama (SAW) kuma wannan gida na freedom ya cancanci mu yaba masa sai dai abin da ya dace muyi shine mu nemi wannan gidan rediyo yayi gyara a bangaren addinin musuluncinsa domin mai shugabantar wannan bangare dan ta adda ne wanda kalmomin bakinsa basu yi kama dana dan jarida ba.Wannan gidan rediyo na freedom a wani lokaci ya taba hira da shugabannin kungiyar da suke adawa da Malam Zakzaky wanda a cikin hirar daya daga cikin wanda ake hirar dashi ya nemi ya taba shaksiyar Malam Zakzaky inda a take wannan gidan rediyo ya dakatar da hirar dashi, wanda wannan abu ya burge ni matuka ashe kenan akwai wadanda suka dace su jagoranci shirye shiryen addinin wannan gida na freedom wadanda ko a ina a duniya za su iya amma sai gashi wannan gida ya baiwa mutumin da ko gidansa ba zai iya yiwa jagoranci na adalci ba shugabantar wannan bangare mai matukar girma da kuma muhimmanci. Ku duba ku ga yadda sauran ma'aikatan wannan gida suke gabatar da shirye shiryensu cikin mutunci da girmama juna hatta masu gabatar da shirin siyasar gidan wancan rediyo da ba su kware ba ai da tuni Kano ta kama da wuta idan kuna shakka ku baiwa Kabiru mai shugabantar sashen musulunci gabatar da shirin ko wane gauta na sati kawai ku ga abin da zai faru.
Ina son hukumar gidan freedom rediyo ta sani duk mutanen da suke yi musu jaje kuma suke kiran wadanda suka kai musu hari da sunan 'yan ta'adda wallahi akasarinsu ba masoyan gidan rediyon freedom ba ne bane ba, domin sun boye musu gaskiya domin abin da ya dace su fadawa hukumar freedom shine su sauya shugaban sashen addini na freedom kuma su hada shi da 'yan sanda domin shi ya jawo musu abin daya same su na asara. Kuma yana da kyau hukumar wannan gidan rediyo da ta dinga la'akari da abin da al'umma suka fi kauna kuma suke akai domin hakan zai kara musu masoya. Shin yanzu ba freedom rediyo ake kiran wancan gidan rediyo ba? Wanda a fassara shine tashar rediyon 'yanci. Shin 'yanzu wannan gidan rediyo na freedom ya baiwa 'yan uwanmu 'yan shi'a hakkinsu inda yake kirawo wasu masu shiga rigar Malamai suna cin zarfin 'yan shi'a wadanda musulmi ne 'yan uwanmu ba tare da ya baiwa 'yan shi'a hakkinsu ba na kirawo Malamansu su kare akidarsu da ba? Ko su 'yan shi'a basu da 'yanci bayi ne? Tabbas gidan rediyon freedom musamman ma'aikatanku wanda bada hakkinsu wannan al'amari ya shafe su ba sai dai Allah ya saka musu su kuma wadanda suka jawo ko nace wanda ya jawo wannan al'amari ina kiransa da yayiwa Allah ya kyalemu da murnar da muke yi na ranar da aka haifi Manzon Allah (SAW), ya kyalemu da wazifarmu da salatin Manzon Allah (SAW) da zikirinmu da yabon Manzon Allah (SAW) din mu. Allah ya taimaki masoyan Manzon Allah (SAW) da iyalansa tsarkaka, amin.
RABIU YUSUF,
KANO.
08065273401.
 

Looking for earth-friendly autos?
Browse Top Cars by "Green Rating" at Yahoo! Autos' Green Center.


Need Mail bonding?
Go to the Yahoo! Mail Q&A for great tips from Yahoo! Answers users.

__._,_.___
Recent Activity
Visit Your Group
Yahoo! Avatars

Make a Virtual You

Show your style &

mood in Messenger.

Yahoo! Mail

Next gen email?

Try the all-new

Yahoo! Mail Beta.

Y! Messenger

Talk it up - free!

Call your friends

worldwide - free!

.

__,_._,___

No comments: