Index

Tuesday, April 10, 2007

[kanoshia] TUNATARWA TARE DA MAULANA ZAKZAKY (H)!!!

Makasudin Makon Hadin Kai


Mai karatu wannan wani jawabi ne da Malam Ibraheem Zakzaky ya gabatar a lokacin da yake ta'aliki ga jawabin da Malam Halliru Maraya ya gabatar a wajen taron Makon Hadin kai da aka gabatar a Fudiyya Islamic Centre, Zariya, wanda kuma aka fara ranar Asabar din da ta gabata kuma aka kammala jiya. Mun dan jingine wancan jawabin da muka soma kawo maku a makon da ya gabata sai wani lokaci nan gaba kadan. Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto mana.
GABATARWA
Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuh. To yau 12 ga watan Rabi'ul Awwal 1428. Kuma wannan shi ne karo na 4 da muke amfani da wannan dama tsakanin 12 ga watan Rabi'ul Awwal zuwa 17 ga watan Rabi'ul Awwal don yin wannan mako na hadin kai. Wannan shi ne karo na 4 a wannan mahalli.
Shi wannan 12 ga watan Rabi'ul Awwal ga ruwayar da ta fi shahara ita ce ta yi daidai da ranar haihuwa Manzon Allah (S). A kuma wata ruwaya wacce ita ta fi inganci, an nuna 17 ne. Don haka duk biyun muka gwama tsakanin 12 da 17 din. Ya zama kwanakin nan biyar akan yi tarurruka irin wannan. Malamai daban-daban daga nahiya daban-daban da ra'ayoyi daban-daban don dai a sami kusanci da juna da fahimtar juna da kara dankon zumunci da hadin kai a takanin al'ummar musulmi.
MANZON ALLAH YA NE YA TSAMAR DA AL'UMMA DAGA HALAKA
Kamar yadda kuka gani yau laccar Shaikh Halliru Maraya ita ce mabudin wannan mako a wannan karo, wanda ya yi magana dangane da hakkokin Manzon Allah (S) a kan al'umma.
Na'am mun takura masa, ganin cewa ba mu fara da wuri ba. Abin da yakan faru shi ne rana takan zama tana da zafin gaske ne, sai muka ga gara ya zama an tunkuda magana din gaf da Magariba don daidai wannan lokacin ya dan fi dadi. To sai ya zama kuma zuwa magriba din ya sa dole an yanke magana din. Amma na san kila da yana da lokaci a yi ta ta yi, da an sha hakkoki daban-daban.
Daga cikin hakkokin ya tunatar da mu wasu muhimmai kamar guda uku ko fiye. Na farko ya fada dangane da 'mawadda', son Annabi da son Iyalan gidan Annabi. Na biyu, ya ce wannan so din yana nufin biyayya ne. Sannan na uku kuma ya kawo batun salati ga Manzon Allah (S) da wadansu hakkoki da ya fada. Wadannan sune muhimmai daga ciki.
Manzon Allah (S) shi ne ya zo da shiriya da addini na gaskiya, wanda ya tsamar da al'umma daga halaka. Kuma ba ya zo ne da sakon nan ya ce ma mutane ga sakonku Allah ya aiko ni da shi in ba ku ba. Alal misali ba ya zo da Alkur'ani ne a rubuce a littafi ya ce, "gashin ku, zancen Allah ne ku karanta, ku shiriya," ya fafi abinsa ba. Ba ya karanta wa mutane ne kuma kawai ya kyale su ba, a'a sakon nan ya zuwa gare shi ne da al'umma baki daya. Saboda haka shi ne farkon mai aikatawa. Sai da ya zama a aikace sai da ya tarbiyyantar da wannan al'umma a kan sakon, ya kuma dauki dawainiyoyi, wahaloli, takalifai wajen ganin ya isar da sakon. Kamar yadda (Shaikh Maraya) ya yi bayani), daga ciki akwai hakuri. Ya daure wa wahaloli wajen isar da sakon nan. Wato ko da a ce ya zo da sakon nan ne ya ce, "gashin ku, in kuka bi wannan za ku tsira gobe kiyama." Ba ya kawo sako ba? Idan da wani zai aiko maka da wata kyauta misali. Hausawa sukan ce yaba kayauta tukwici! Ka ga shi ya zo ne ya ce maka ga shi kawai an aiko shi da shi ya ba ka ya tafi abinsa. Ko da kamar misali wata na'ura ce, sai kuma ya zauna yana nuna maka yadda za sarrafa ta, ya tabbatar ka iya sarrafa ta tukuna kafin ya tafi.
DA WANNAN SAKON DA MANZON ALLAH DUK ABU GUDA NE
Shi Manzon Allah da ya zo, ko da sakon kawai ya kawo ya cancanci a yaba masa, to ballantana kuma sai ya sha wahala wajen ganin ya isar da sakon. Ya sha wahala aka azabtar da shi shekaru goman Makka, aka kore shi daga garinsu, aka bi shi da yaki aka yi masa rotsi, aka ji masa ciwo har ta kai ma ma akwai lokacin da ya yi sallar Azuhur da La'asar a ranar Uhud, bai iya yi a tsaye ba. Manzon Allah ya sha wuya ba karamar wahala ba wajen ya ga ya isar da sako din nan. Har sakon ya tabbata. Ya zama bai bar duniya ba sai da ya ga cewa ba kawai ya isar da sakon ne ta hanya ya gaya mana komai ba, sai da ya ga ya dora mu a kai, sai ya dora al'umma al'umma a kai sannan ya tafi ya zuwa ga rahamar Ubangijinsa.
To yanzu wannan ya zama shi kenan nasa kenan an gama? Ai ya cancanci mu kuma ya zama akwai wata dawainiya da za mu yi wajen godiya ga irin aikin da ya yi. Ta wannan za ku fahimci wadansu mutane, kamar dai shi Shaikh Halliru yana masa addu'a ne, haka ya dace, wasu mutane sai suna kamanta shi da cewa ai shi ba shi da muhimmanci, shi nasa isar da sako ne kawai. Har ma wani wai shi ko yana ganin yana da hikima ne, ya ce misalin Annabi a wurinsa kamar ambulan ne aka saka wasika, to in aka ba ka wasikar in ka ciro wasikar, sai ka yarda ambulan din. Wato shi ya zo da sako ne kawai, wato ma'ana shi kawai fanko ne aka sako sako aka kawo masa, shi kenan. Kuma ibada kana yi ya zuwa wajen Allah ne, ba ruwanka da shi Manzon Allah. To wannan ba haka bane, shi wannan sakon, da shi da Manzon Allah din duk abu guda ne. Da sakon da Annabi, abu daya ne.
Da mutum zai tankware darajar Annabi kadan, to kuma ya rusa sakon dari bisa dari ne. In da zai tankware ma Annabi daraja kalilan, to ya kuma rusa sakon shi Musuluncin dari bisa dari ne. Ba ya dan tankware Musuluncin bane, ya rusa shi ne, saboda ba Musulunci in ba Manzon Allah. Shi ne sakon, saboda shi ne sakon a aikace. Shi ne aka ajiye mana samfur wanda za a gani a kwafa. Shi ne misali wanda za ka ce masa kammalallen misali. In da akwai wanda za a ce masa kamili, to shi ne kamili, shi ke da kamala. Ba za a kai ya shi ba, amma shi za a kwafa.
Saboda haka ka ga yana da wasu hakkoki wanda ya wuce kawai a dube shi a matsayin mai sako. Kuma Allah (T) ya sanar da mu dukkan Annabawa sun fadi wani zance guda daya wanda ya kamu, cewa ba haraji. "An tas'aluhum alaihi ajran fahum min makrimin muskalun." Cewa Allah (T) yana ce masa " ko ka ce masu su biya wani lada suna ganin da nauyi su biya wannan harajin." Za ka ga kowane Annabi ya ce "wa ma asa'alukum alaihi ajran, in ajriya illa ala Rabbil alamin." Haka Annabi Nuhu ya fadi, haka Annabi Shu'aibu ya fadi, haka nan Annabi Salihu, haka nan sauran duk Annabawa suka fadi, "wa ma as'alukum alaihi ajran in ajriya illa ala Rabbil alamin."
To wannan shi Manzon nan shi ma haka nan. A wurare da dama za ka ji yana cewa ban tambaye ku lada ba. Sai a nassin da shi Shaikh Maraya ya kawo a kan cewa sai Allah (T) ya ce, a'a akwai lada. Wannan ba shi Annabi ne ya ce a ba ni ladan ba, shi Allah (T) ne ya ce ka ce masu. "Kul la as'alukum alaihi ajran." Ka ce ba na tambayar ku lada a kan shi, wato wannan sakon, isar maku da sakon nan. To sai Allah (T) ya ce "illal mawaddata fi kurba." Ka ga ashe akwai ladan kenan ko? Ka ga akwai ladan kenan!
Wannan lada ba in kun bayar kun biya lada kenan kun huta ba, a'a wato wani karin falala ne gare ku, domin in kun bayar sai kuma Allah (T) ya kammala maku ladanku, na aikinku. Na'am haka Allah (T) ya kira shi lada, sai ya ce, to wannan ne kawai.
Wato da misali, wanda ya kawo mana wannan shiriya, wanda yake tsamar da mu daga bata, zai zama ya yi nauyi in aka ce, to bayan haka nan, in ka yarda da wannan ita ce gaskiya? Eh, wannan shi ne addini na gaskiya? Shi ya tsamar da kai daga halaka ya kai ka ga tsira? To yanzu ya rage abu guda. Ka ce, mene? A ce ai ana ciro kunni ne na dama. Ai ina ganin da sauki ai, sai kawai ka ba da kunni a cire, da sauki. Ko kuma ai kunnuwa ake cirewa duk biyu. Ko kuwa ai hanci ake gutsurewa, ko kwakule ido ake yi. Duk za ka ce ai ya yi sauki. In ce ko ba zan shiga wuta ba? A ce eh, ka ce to a cire idon. To sai aka ce duk ba wannan, ba a ma ce ka ba da ko kwabo ba, ba haraji, sai aka ce abin da ake so kawai, ka so wannan Annabin, ka so Iyalan Annabi, shi kenan.
ABIN DA AKE NUFI DA 'AHLUL BAITI'
'Mawaddata fil kurba' din nan, Manzon Allah ya yi bayani. Don ana ta bayanin Ahlul Baiti, ana ta bayanin Ahlul Baiti, ta yiwu mutum ya dauka abin da ake nufi da Ahlul Baiti su ne Kuraishawa, ko kuwa sune Hashimawa, ko kuwa sune Sharifai ko 'ya'yan Hasan da Husaini har ya zuwa ranar alkiyama, a'a. Wadansu ayyanannun mutane ne wadanda yake Manzon Allah ya siffata su da cewa za su juya da littafi duk inda ya juya, ba za su rabu da littafi ba har su hadu da shi a koramarsa gobe kiyama. Wadansu ayyanannun mutane ne, su ne 'A'imma,' sune 'Ma'asumin!' Sune wadanda Allah (T) ya kawar da kazanta daga gare su, bai taba shafar su ba. Ba wai suna da kazanta ne ya cire ba, ya kawar da shi ne daga barinsu, ya tsarkake su tsarkakewa. Sune suka shiryar da mutane a kan tafarki.
To mun san siyasar duniya wacce ta haifar da abubuwa, wanda daga baya aka maishe shi cikin addini, 'wa'iyazu billahi,' ya haifar mana da masifofi da yawan gaske. Na ji ya kawo wani hadisi na Manzon Allah wanda yake cewa 'wanda ya so Hasan da Husaini da Uwarsa da Ubansa, zai kasance tare da Manzon Allah a darajarsa.'
Aka ce wannan hadisi, akwai wani Khalifa. Sai ya tunatar da ni, wani Khalifa ya kamo wanda ya fadi wannan hadisi. Don ba a yin wannan hadisin, Khalifofi sun hana. Ya yanke masa bulala dubu saba'in, haka aka dinga fyada masa.
Kun san a shari'a, ta'aziri iyakarsa bai zai kai bulala tamanin ba. Mafi yawan ta'aziri ba zai kai mafi karancin haddi ba. Mafi karancin haddi bulala tamanin. Saboda haka mafi yawan ta'aziri ba zai bulala tamanin ba, dole in ya yi tsanani ya kai bulala tamanin da tara. To shi dubu saba'in ya yanke masa. Kuma haka aka yi masa bulalar.
Wato an hana cewa kar ma a yarda a san su wane ne aka ce Ahlul Baiti din nan, kar kuma a yarda a bi su. Saboda mene? Sarakan wadannan lokuta suna ganin in aka ce akwai wasu na hakki na a bi su, to a bu su Sarakai? To shi ne dalili. Shi ya sa kuma Sarakai suka ga cewa sun bullo da hanyoyi irin nasu, suka kirkiro hadisai da littattafai da sauransu don a nuna kowa da kowa ma wannan darajar da Allah ya ba wadansu kebantattu, na kowa da kowa ne. Wannan shi ya haifar mana da shubuhohi a addini.
ABIN DA MANZON ALLAH YA YI DA YA GA MUTANE A KAN BATA
Amma kamar yadda nake cewa mutane ma'azurai ne. don Allah (T) gobe kiyama zai yi wa mutane hukunci ne da daidai gwargwadon iliminsu. Don haka ne ma muke ganin cewa idan da ka fahimci gaskiya kuma kana ganin kai ma'abucinta ne, ka san ta, kana ganin kuma wadanda ba su a abin da kake a kai, suna kan bata ne, me ya kamata ka yi ma sauran mutane da kake ganin su a matsayin batattu? Ka ce masu 'ya ku batattu?' 'ya ku 'yan wuta Kafirai?' Ba za ka so su da shiriyar da Allah ya ba ka ba? Abin da muka ga Manzon Allah ya yi kenan. Duk da wahalolin da ya sha a Makka da Madina, da irin gana masa bala'in da aka yi, amma duk da haka shi daurewa ya yi yana neman mutanen nan su shiriya. To wannan yana daga cikin alamar masu kira ya zuwa ga tafarkin Allah.
Duk wanda ka ga yana cewa shi yana kan gaskiya ne, amma yana ta fushi yana ta kunduma ashar, yana ta fada da sauran al'umma, to ba salon kiran Manzon Allah ba kenan, kuma bai kama da a kan gaskiya yake ba. Domin inda a kan gaskiya yake ba zai rasa komai ba in wasu suka shiriya, abin da ma yake so kenan. Maimakon ya yi fada da su, kamata ya yi ya kira su.
Muna ganin wannan dama ce muke ganin abin da ya kamata, in ma mutane sun dauka yadda ake yi a musulmi akan ta rigingimu ne tsakanin wannan da wannan, wannan ya ce su ne 'yan kaza wadancan 'yan kaza. To wannan dama ce da muka samu, duk da dai mun hada shi da mauludi, wasu kuma sun ce Mauludin sun ce ba kyau, muka ce masu ko da ka dauka Mauludi ba kyau, don Allah ka zo wannan, ka dauka shi wannan yana da kyau, saboda shi wannan za mu yi magana ne kan hadin kai. Kai ka zo da batun kana wa'azin hadin kai ne ba ruwanka da mauludi, ka ga ba ka yi bidi'a ba, ka huta. Sai kawai a zo a yi magana kan batun hadin kai da fahimtar juna. Mu kuma masu bidi'a mu mun san ladan bidio'armu insha Allahu. Mu da muke bidi'ar Mauludi, insha Allahu, Allah ba mu ladan mai yawan gaske. Kai kuma ka huta da ladan ladar bidi'ar, ka ga ka huta, ba ka da shi.
ABIN DA MUKE NUFI DA HADIN KAI
To amma akalla dai tun dai hadin kai ne, a gane cewa. Kullum muna nanata wannan maganar cewa idan muka ce hadin kai ne, ko miskala zarratin ba muna nufin mutum ya bar fahimtarsa da ra'ayinsa da ganewarsa ya zo namu bane. Abin da muke cewa shi ne a kusanci juna, a kawar da wadansu abubuwa da makiya za su so ya zama akwai. Domin mun fahimci cewa nisantar juna din yana amfanar makiyanmu ne. Har makiyanmu sun gano, suna bukatar mu mu yi surutu ne na fada da juna su kuwa su sa makami. Yanzu abin da suke yi a Irak kenan.
Su makami suke sa wa. Ba wani ke sa bama-bamai din nan, ka ji an ce wadannan sun jefa wa wannan, wadannan sun jefa a masallacin wadancan, wadannan sun jefa a masallacin wadancan, illa wadannan mutanen da suka mamaye kasar. Su suke yin wannan aikin. Amma kullum sai su ce wannan ne ya rama gayya. Sai su yi ma wannan su ce wannan ya rama gayya, ba sai na gaya maku wane da wane ba. Ko a labarai kun ji ana fadi.
Ko shekaran jiya kun ji. Shekaran jiya wancan an kai hari a gidajen kwanan mutane, an ta da bom ya kashe mutane sittin da 'yan kai har da jarirai, ana ta fito da su a Baraguzan gini. To shekaran jiya kuma sai aka ce ga shi nan an mai da martani, su ma 'yana wadancan ne a unguwar 'yan wadannan. Ba sai na ce su wanene ne ba. Su kuma sai aka kai hari a unguwar 'yan wadancan, wadanda suka kai din, domin mun san ko su waye suke kaiwa, sai suna fada a kafafen watsa labarunsu, sun kai ramuwar gayya, yanzu su ma sun kashe hamsin da 'yan kai.
YAU SHEKARMU WAJEN 100 DA MAMAYA
Wato kenan idan ku za ku iya magana, to makiyanku za su yi aiki ne. Tana iya yiwuwa kuma a sami wadansu wadanda za su fada tarkonsu. Kamar in sun yi barna sun ce su wane suka yi masu, su ma su ingiza su su je su mayar da martani. In sun mayar da kadan, su kuma sai su kara da yawa, sai abin ya ci gaba a haka nan. Sai ya amfani makiyi. Shi makiyi ya ga cewa kun yi rauni, shi kuma danniyar da ya yi maku ya ba shi dama a kan ya dawwama.
Ko ba komai a wannan kasa, in kai kana tunanin Amerika ta mamaye Irak, mu yau shekarmu wajen 100 da mamaya, a karkashin mamaya muke. Tun yaushe 'British' suka mamaye nan? Yau shekara 100 da 'yan kai. Tun farkon karnin da ya wuce na bature, 1900, har 19 din ya kare an shiga 2000, yanzu ana 2007. To ka ga yau shekara wajen 107, mu muna karkashin mamaya ne. Har sun canza mana harshe, yanzu wai mu Turawa ne, wai Turanci ne 'official language' din mu. Sun canza mana akibla, sun canza mana nizami. Abin da ba su iya yi a Irak da sauran wadansu kasashe ba, wanda yanzu suke so su yi. Wanda mu sun dade da yi. To tuntuni muna mamayar ne.
Yanzu a daidai wannan lokaci a ce kai abin da kake tunani shi ne babban abokin fadanka shi ne dan uwanka musulmi. Kaico! Abin takaici ne. Kamata ya yi al'ummar musulmi su gane da cewa mafitarsu na addininsu ne. Addinin nan shi ne daukakarmu, shi za mu rike, shi ne kuma zai kwace mu duniyarmu da lahirarmu. Wannan kuma ba zai taba yiwuwa a irin wannan hali na zubargada, makiyi na iko ku kuma kuna fada ba.
Wannan shi ne makasudin wannan taro namu. Da fatan Allah (T) ya hada kan al'ummar musulmi, ya sa mu gane da juna, mu fahimci juna. Ya dora mu bisa koyarwar wannan Manzo (S), ya dawo mana da addininmu, ya yi iko da mu kamar yadda ya yi iko da wadanda suka gabace mu. Ya nuna mana lokacin da tutar 'la'ilaha illallah' za ta filfila a wannana nahiya tamu. Ya zama ba za a gudanar da komai a kan rayuwarmu ba sai an ce Allah ya ce Manzon Allah ya ce. Wassalmu alaikum warahmatullahi wabarakatuh.

  |


Food fight? Enjoy some healthy debate
in the Yahoo! Answers Food Drink Q&A.

__._,_.___
Recent Activity
Visit Your Group
Yahoo! Avatars

Express Yourself

Show your style in

Messenger & more.

Yahoo! Mail

Get it all!

With the all-new

Yahoo! Mail Beta

Y! Messenger

Make free calls

Call PC-to-PC

worldwide- free!

.

__,_._,___

No comments: