Tuesday, April 10, 2007

[kanoshia] MALAM, MALAM NE !!!

Malam, Malam ne (2)


Ci gaba daga makon jiya.
Ina fatan Allah ya tsare mana kafofin yada fikirar Malam a duniya don jama'a su amfana da wannan dimbin baiwa. Misali kamar matsalar Iraki, Malam cewa yake da 'yan kasar za su hadu su yaki 'yan mamaya, su kore su daga kasarsu, shi ne kawai maganin matsalar Iraki. Kamar abin da Muktada Sadr ya yi, shi ne kawai mafita. La gairu.
Bisa gaskiya muna so mu kawo sauyi ne kan duk wani fanni na rayuwar mutanen wannan al'umma tamu. Ta fannin ilimi da malanta. Ai a duk duniyar musulmi, da Malami da dalibai, al'umma ce ke daukar dawainiyarsu. Mu ma da izinin Allah muna fatan daukaka martabar ilimi ta hanyar daukar dawainiyar ilimi da malanta. Allah kuma ya taimake mu a kan wannan.
Wasu abubuwa da aka bijiro da su ko ambata a rubutun farko, don a sani ba hukunci muka yi da su ba, kamar mafarki da muka ambata. Ai mafarki mai kyau in mutum ya yi, sai ya roki Allah ya tabbatar masa da shi; in kuma mara kyau ne, sai ya roki tsarin Allah. Na yarda da cewa kowa yana da alhakin aikinsa da ya aikata. Kuma bai kore mutum ya jingina wa Allah wani kyakkyawan aiki ba wanda ya nufe shi da yi.
Wannan makaranta ta iyalan gidan Manzon Allah (SAWA) ta koyar da mu mu yi kira mutane zuwa gare su ba da harshenmu ba. Wato kyawawan ayyukanmu su zama shi mutane za su gani ya burge su, sai ya zama ta wannan hanya sun fahimci makarantar iyalan gidan Manzon Allah. Tirkashi! Wannan da ban tsoro. Ni dai abubuwan da ake fada ko rubutawa na suka da wasu suke yi mana babu ladabi, girmamawa da mutunta juna; kuma wannan bai dace ba. Kada ya zama garin kokarin yin hidima ga wannan tafarkin, muna yin saddu ne a tafarkin iyalan gidan Manzon Allah, su kuma rike mu da shi gobe kiyama.
A fagen tarbiyyar yara, Malam ya yi nisa, don ko tsakaninsa da 'ya'yansa akwai girmamawa. Yana musu wasa da dariya. Na taba jin ya ce tunda ya karanta cewa Manzon Allah ya hana dukan yara, to bai taba dukan su ba. Yana kula da iliminsu na addini da na boko.
Akwai hadisin da ke cewa mafi alherinku sune wadanda ke amfanar da mutane, wadanda rayuwarsu ke amfanar jama'a, ko kuma Malami wanda ke ilmantar da jama'a. A duk wannan mahanga mutane na amfana da Malam, musulmi da wadanda ba musulmi ba. Ya koya wa mutane fada da zalunci, da rashin jin tsoron azzalumai da iya cewa na ki yayin da aka yi abin da ba su yarda ba. Madallah da wannan rayuwa ta Malam.
Ana zargin mu da cewa 'yan uwa almajiran Malam sun kirkiro wata sabuwar da'awa, ko kuma ta bakinsu 'Shi'a sabuwa.' Ba haka bane. Gaskiyar magana ita ce duk da Jafariyya muke, amma muna da jagoranci da muke yi wa biyayya. Kuma wannan shi ne ya bambanta mu da sauran jama'a. Da yake hatta a fannin addini ana sa Nijeriyanci, su kuma 'yan uwa sun yi kokari sun yaki Nijeriyanci, sun magance ta. Sauran mutane kuma tunda akwai tasirin wannan a rayuwarsu ta yau da kullum sun kasa fahimta. Ta fuskacin ladabi da biyayya ai 'yan uwa sun yi wa sauran mutane nisa.
Na san wani Malami da ya ziyarci Malam, bayan da ya koma sai yake bai wa wani labari cewa, lalle yadda ya ga 'yan uwa suke yi a gaban Malam a natse, ya tuna masa da labarin sahabbai, wadanda aka ce in suna gaban Manzon Allah (SAWA) kamar da tsuntsu a kansu.
Abin da muke cewa shi ne, Malam, Allah ya yi masa baiwa, kuma wannan baiwar da ke tare da da shi ita ce ta sa shi abin da yake yi da kuma abin da ya zama. Wanda yake ganin cewa kokarinsa ne ya maishe shi haka, to ga kule gare shi! Shi ma ya yi kokari mana ya zama! Inda babu kasa, ai nan ake gardamar kokawa, in ji masu iya magana. Kuma ga fili, ga doki! A gwada mu gani!!
Wani Bature Bajamushe (dan Jamus) ya zo gidan Mala ya ce ya zo ne saboda su tattauna, ba 'interview' ya zo yi ba. Don yana karanta 'interview' na Malam kuma yana ganin 'analysis' (bayanai masu zurfi), kuma suna burge shi. Saboda wannan ne ya zo su tattauna don ya amfana. To, ka ji, yabon gwani ya zama dole.
Duba ka gani yadda Malaman Shi'a da Sunna suka fada tarkon Amerika bayan da suka kashe Saddam Husain. Da ma makasudin wannan aikin nasu shi ne sun aukar da rikici tsakanin Shi'a da Sunna. Kuma lalle sun fada wannan tarkon. Amma su Malam sun fayyace matsalar tsaf. Ya ce, "Wannan wata dasisa ce ta Amurka, kada musulmi su fada." Muna godiya ga Allah da ya mayar da mu almajiran wannan Masanin – Zakzaky. Allah ya kare shi, ya bar mu tare da shi.
Na san cewa akwai wani lokaci da Sayyid Ka'id Khamene'i ke ziyarar gidajen shahidai, an fito za a nufi wata unguwar shahidan, sai ya ce ba nan za su nufa ba, a nufi wani wurin na daban, amma shi ma gidan wani shahidi ne. Suna zuwa gidan wannan shahidin sai iyalinsa ta shaida musu cewa jiya ta yi mafarki da Manzo (SAW) ya ce mata Sayyid zai ziyarce ta a yau. To, ka ji! Menene dalilin da ya sa mu in muka ce wani dan uwa ya yi mafarki da Manzo (SAWA) ya ce masa ya bi Malam sai ka zarge mu?
Sannan zancen cewa lokacin da Imam Khomeni ya tunkari wacce zai aura da maganar aure, sai ta ki amincewa da bukatarsa. To amma sai ta yi mafarki da Sayyida Zahra da Imam Ali sun bata rai, sun nuna rashin gamsuwa da abin da ta yi. Ai sai ta amince da bukatarsa, sai suka yi aure. To yaya dai? Ka ji duk shi'arka dai ba ka kai su ba.
Mutanen garin Ankpa sun gayyaci Malam ya je ya shaidi rantsar da sabbin dalibai (matriculation) da bude wani dakin taro da aka yi wa lakabi da 'Sheikh Ibraheem Zakzaky Hall' da aza harasashin ginin wasu 'Theatres' (dakunan karatu) na Danfodiyo, Imam Khomeni da Zakzaky na al-Hikima College Of Education Ankpa, na al'ummar musulmin Ankpa. Malam ya halarci wannan makarantar, kuma ya yi duk wadannan abubuwan da muke ambata. Abin da ban sha'awa. Kuma kule ga mutanenmu, in fa ba a shirye muke mu yi addinin ba, to Allah zai musanya mu da wasu. Kuma mutanen 'Igala land' kam sun yi 'azama' (himma) don taimakon addinin Musulunci, manyansu da yaransu, kai Malamansu har da su; abin da ban sha'awa.
Kuma Malam shi ne babban bako mai jawabi a makarantar, ya kuma yaba da kokarinsu da himmarsu na assasa wannan makaranta. Ya kuma yi musu fatan Allah ya sa nan gaba su maishe ta jami'ar Musulunci. Ya kuma ba su gudummawar dubu hamsin da kwamfuta daya.
A wasu lokutan baya Malam ya ziyarci garin Lokoja, inda ya ziyarci kaburburan wasu Sarakunan Musulunci da Bature ya kai su garin Lokoja suka rasu a can, irin su Sarkin Kano Aliyu Abdullahi, Sarkin Zazzau Aliyu Dan Sidi da su Sarki Kwasau da Sarkin Bida da na Gwandu.
Sad da Malam ya je da farko, duk wadanan kaburburan sun zama bola da wurin kewayawa da gidajen bera da burgu, an manta da su, musamman ma na Sarkin Kano. To amma cikin hukuncin Allah zuwan Malam ke da wuya sai kowace masarauta ta tashi haikan da gyara makabartun Sarkinsu. Na Kano dai sun yi nisa, an gine wurin, an yi azuzuwa, kuma an kewaye wurin.
Na Zazzau su ma ba a bar su a baya ba. Sun gina masallaci a wurin kabarin Aliyu Dan Sidi da wasu azuzuwa. Nasu dai akwai sauran aiki.
Kafin ziyarar Malam Zakzaky wadanan kaburburan lallai an manta da su, don kafin ka shiga wurin sai ka rufe hancinka don wari da kazanta.
Wannan abu da na gani a Lokoja na sanya shi cikin nasarorin Malam Zakzaky. Bisa gaskiya in Malam ya je wuri, to 'analysis' ake yi shin menene dalilin zuwansa? Me ya ce? Da sauransu. Su kuma yi kokarin samar da amsoshin wadannan tambayoyin. Aka ce Malam kyaran wasa. In ka ji an ce ki gudu, to sa gudu ne bai zo ba. Kuma canji na yiwuwa daga waje. Ga shi ya yi mun gani. Allah ya bar mu tare da Malam. Labbaika!
A lura wannan rubutun amsa ne na yi wa wani da ya yi mini martani. Kuma na yi kokari ne na ba shi amsoshin duk abin da ya ce ba tare da na ruwaito abin da ya ce ba saboda wasu dalilai.


  | 


Bored stiff? Loosen up...
Download and play hundreds of games for free on Yahoo! Games.

__._,_.___
Recent Activity
Visit Your Group
Yahoo! Avatars

Create a Face

Show your style in

Messenger & more.

Yahoo! Mail

Get it all!

With the all-new

Yahoo! Mail Beta

Y! Messenger

Group get-together

Host a free online

conference on IM.

.

__,_._,___

No comments: