Monday, April 9, 2007

[kanoshia] Malam Ibrahim Technical ya koma ga Mahallicinsa

Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un
           Malam Ibrahim Technical ya koma ga Mahallicinsa
Daga Wakilanmu
 
A ranar Juma'ar ta gabata ne Malam Ibrahim Jibril (Technical), tare da wasu 'yan uwa su biyar suka riga mu gidan gaskiya sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da su kimanin kilomita 15 kafin su shiga darin Dukku na jihar Gombe.
Hadarin dai ya auku ne da misalin karfe 11:30 na dare lokacin da tayoyin motar biyu suka fashe, inda motar ta rinka mirginawa sai da ta juya har sau uku.
Kamar yadda daya daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su ya shaida wa ALMIZAN, tuntsurawar da motar ta rinka yi da su ne ya jawo ta rinka watso su waje tana dannewa, inda kuma wasunsu suka rasu, wasu kuma suka samu munanan raunuka.
Sauran wadanda suka rasu sun hada da Malam Sadisu Dan Dishe, 38, Malam Shi'ithu Kurna, 35, Malama Maryam Sani Bala Dakata, 53, da kuma Ahmad, 3, da wata budurwa da ba mu sami sunananta ba.
Wadanda kuma suka samu raunuka sun hada da Sani Doka, Ahmad Yusuf, Sulaiman Kurna, Nura Bachirawa, Basiru Sani, Husaini Musa da kuma wasu mata uku.
Tuni dai aka yi jana'izarsu, wacce Malam Muhammad Turi ya sami halartar wani bangarenta.
 


Looking for earth-friendly autos?
Browse Top Cars by "Green Rating" at Yahoo! Autos' Green Center.

__._,_.___
Recent Activity
Visit Your Group
Yahoo! Avatars

Share Your Style

Show your face in

Messenger & more.

Yahoo! Mail

You're invited!

Try the all-new

Yahoo! Mail Beta

Y! Messenger

Group get-together

Host a free online

conference on IM.

.

__,_._,___

No comments: