Tuesday, April 10, 2007

[kanoshia] MAKON HADIN KAI YAYI ARMASHI!!!

Taron Makon Hadin Kai da irin natijar da ya haifar


Daga Aliyu Saleh
Dogon layin jama'ar da ke burin shigar farfajiyar harabar Fudiyya Islamic Center da ke Dan Magaji Zariya don sauraron jawaban da Malamai ne mutum zai fara yin tozali da shi a daidai lokacin da ya karya kwanar shiga wajen da ake gudanar da taron Makon Hadin Kai na kwanaki biyar da Harkar Musulunci karkashin jagorancin Malam Ibraheem Zakzaky ta shirya.
Taron, wanda shi ne karo na hudu, ya haifar da wasu natijoji da kuma wasu karin fa'idodi da ba a samun su a waninsa. Malamai da dalibansu daga ra'ayoyi, kungiyoyi da fahimtoci daban-daban sun kusanci juna, sun ji daga juna, sun saurari ra'ayoyi da fahimtar juna. An samu karfin kusanci da sakankancewa da juna.
A ranar Asabar, wacce ita ce ranar farko ta fara wannan taron, an samu halartar Shaikh Halliru Maraya, wanda Malami ne da tauraruwarsa ke matukar haskawa, musamman a tsakanin 'yan Darikar Tijjaniyya, ba kawai saboda dimbin ilimin addini da na bokon da ya tara ba, amma har da burin da yake da shi na kau da katangar karfen da babu ita da aka gina a tsakanin Musulmi.
A cikin jawabin da ya gabatar mai taken 'Hakokkin Manzon Allah A Kan Al'umma' ya nuna hakan a zahiri, inda ya bayyana hadin kai da fahimtar juna a matsayin wani wajibi daga cikin wajibojin addinin Musulunci.
Ya ce muhimmancin hadin kai ya zarce duk yadda mutane ke tunaninsa. Don haka ma sai ya yi jinjina ta musamman ga wadanda suka yi tunanin shirya wannan taron na Makon Hadin Kai. "Duk wanda ya gayyace ka mauludin Annabi (S) ya gama yi maka komai na shaida."
Ya ce da al'ummar musulmi sun yi riko da koyarwar Manzon Allah (S), ba wani kai-ruwa-rana, domin Manzon Allah (S) ya dora mutane a hanya yadda ya kamata. Ya nuna waye musulmi wanda ya wajaba su tafi tare. "Da mun dauki duk wanda muka gan shi yana salla musulmi da ba mu samu rarrabar da muke fama da ita a yanzu ba."
Malamin ya yi dogon bayani a kan maudu'in da aka ba shi, kamar yadda kuma ya yi masa adalcin da ya kamata. Mutanen da suke wajen da muka zanta da su cikin natsuwa, tare da jin dadi, sun nuna matukar gamsuwa game da jawabin na Shaikh Halliru Maraya.
A ta'alikin da ya yi wa jawabin na Shaikh Maraya, Malam Ibraheem Zakzaky, ya bayyana abin da ake nufi da hadin kai. Ya ce hadin kai ba shi ne kowa ya bar abin da yake yi, ya zo ya yi na wani ba. Da yake dama samun bambanci a tsakanin mutane lazim ne, amma kusantar juna da kuma nisantar fadace-fadace da kuma sassabawa ake nema.
Ya ce katangar karfen nan, wacce babu ita da makiya suka gina a tsakanin musulmi ake so a kawar. "A zahirin gaskiya ma dai ba wani sabani a tsakanin al'ummar nan." Ya ce nisantar juna yana amfanar makiyanmu ne. Ya ce su suna bukatar mu yi surutu ne su kuma su yi amfani da makami a kamu. Ya ba da misalin abin da ke faruwa a Iraki a yanzu.
Malam ya ce Manzon Allah (S) shi ne wanda ya zo da shiriya ya tsamar da mutane daga halakar da suke ciki. Ya ce Manzon Allah sai da ya sha wahala wajen isar da sakon da ya zo da shi. Ya ce da Manzon Allah (S) da sakon duk abu daya ne. Ya ce ba Musulunci in ba Manzon Allah (S), shi ne sakon a aikace. Ya ce Manzon Allah (S) yana da hakkin da ya zama wajibi a kan al'umma.
Da dare ma kamar da rana, muhallin taron Makon Hadin Kai ya yi cikar kwari ba masaka tsinke don sauraron jawabin da zai fito daga wani fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan da ya yi suna wajen shigo da mutane addinin Musulunci a karkashin inuwar Kungiyar Izalatul Bidi'a wa Ikamatus Sunna, Shaikh Lawal Sule Abdullahi Zariya.
Shaikh Lawal Sule mutum ne da ya goge a fannoni daban-daban. Duk da cewa ya yi wa maudu'in da aka ba shi na 'Wabijcin Riko Da Alkur'ani' shigar shantun kadangare, amma ya yi masa duk adalcin da ya kamata, inda ya fito da duk abin da ake nema cikin raha da nishadantarwa.
Shi ma kamar wanda ya gabace shi, ya bayyana matukar jun dadinsa da wannan taron da aka kira na Makon Hadin Kai. Har ma ya ce ta hanyar yin riko da Alkur'ani ne ake samun cikakken hadin kai a tsakanin al'ummar Musulmi. Ya ce wajibi ne a samu irin wannan hadin kan da ake nema matsawar musulmi na so su kwashe da mara.
Ya nuna muhimmacin ware lokaci na musamman don a yi tattanawa ta musamman a tsakanin al'ummar musulmi har a gano dalilan da suka sa Dan Izala ke sukar Dan Darika, Dan Shi'a ke sukar Dan Izala, ko Dan Darika ke sukar Dan Izala. Ya ce dama Allah ya fada a cikin Alkur'ani, idan aka samu 'tanazu'i' a tsakanin al'ummar musulmi sai a mai da al'amarin ga Allah da Manzo don su warware matsalar.
Sai dai kuma Malamin bai kammala jawabin nasa ba, wanda ke cike makil da ilmantarwa da kuma fadakarwa sai da ya nuna kaikayin da suke ji game da ware wannan lokacin na Mauludi domin neman hadan kan Musulmi. Ya ce, "mu 'yan Izala muna ganin Mauludi fa bidi'a ne." Ya kamata a ware wani lokacin da duk al'ummar musulmi suka yarda da shi, kamar lokacin bukukuwan salla, ko sabuwar shekara domin a rinka gudanar da taron neman hadin kan al'ummar musulmi.
Kafin ya bayyana Alkur'ani a matsayin babbar mu'ujizar Annabi, sai da Shaikh Lawal Sule ya hakikance cewa lalle Alkur'ani ne ya wajaba ya zama hanyar rayuwar al'ummar musulmi ba wani tsarin na daban ba. Ya kuma jero irin tarin matsalolin da Alkur'ani ya warware a baya, da kuma yadda zai ci gaba da warware su a nan gaba. Ya ce ba wani ilimi, fasaha, falsafa da dabara da Alkur'ani bai zo da ita ba. Ya ce duk wani da yake ba da wani tsarin ilimin da ba na Alkur'ani ba shirme ne. "Don haka wannan Alkur'anin wajibi ne a yi riko da shi."
A wannan zaman ma Malam Ibraheem Zakzaky yana wajen, kuma ya yi karin haske kan wasu batutuwa da Malamin ya tabo. Ya nuna muhimmancin hadin kai a tsakanin al'ummar musulmi. Ya kuma kore duk wani shaci-fadin da wasu ke yi na cewa wasu suna da Alkur'aninsu na daban na sauran al'ummar musulmi. Ya ce duk wanda yake fadin hakan ya jahilci sakon da Manzon Allah (S) ya zo da shi, domin kuwa Allah ya yi alkawarin kare wannan sakon.
Malam Zakzaky ya nuna damuwarsa a kan yadda duk da ga Alkur'ani a hannun al'ummar musulmi, amma suna zama da wadanda ba su da su da wata mafita suna neman mafita gaba daya. Ya ce rashin yin riko da Alkur'ani da kuma rarrabuwar da ke tsakanin musulmi ba kawai hasara ce a gare su ba, amma har da wadanda aka dora masu hakkin su shiryar da su.
Ya sake nanata cewa ba wata rarraba da ke tsakanin al'ummar musulmi wacce za ta sa ba su za su iya haduwa su yi wa addinin Musulunci aiki gaba daya ba. Domin kuwa duk musulmi sun yarda da Allah, Manzon Allah, Alkibla, da Alkur'ani. Sun kuma hadu a kan salla har ma da yawan raka'o'in. "Muna fatan daga yanzu za a fara kawar da shamakin da ke tsakanin al'ummar musulmi har a samu fahimtar juna, har ya zama ba za a yi komai ba sai an tuntubi Allah da Manzonsa."
Haka aka tashi a ranar zama na farko cikin farin cikin da annashuwa, tare da shan alwashin za a je a yi nazarin abubuwan da aka ce don a ga ta ina za a bullo wa matsalolin da ke ci gaba da ci wa al'ummar musulmi tuwo a kwarya.
A rana ta biyu ta wannan taron, ya dauki wani sabon sallo, domin kuwa tun daga masu jawabin da kuma mahalartan kowa ya samu wani shu'uri a tare da shi, ba kawai don abubuwan da aka fada ba, har ma da irin karfin fahimtar junan da aka gani, gami da ganin wasu fuskokin da ba kasafai ake ganinsu a inuwa daya ba.
Mashahurin Malamin addinin Musuluncin nan da ke Kano, Shaikh Dakta Yusuf Ali, wanda mai gabatarwa, Malam Mukhtar Sahabi ya ce ba ya bukatar gabatarwa ga wadanda suke halarce a wajen taron, shi ne ya fara gabatar da wani jawabi wanda ya bar kowa cikin tunanin yadda zai gano bakin zaren.
Taken jawabin nasa shi ne, 'Makircin Yahudawa'. Da yake Malamin ya kware a wajen iya fito da abubuwa da kuma bayyana su yadda suke ya tsima mahalarta taron, tare da jefa su cikin kogin tunani.
Da yake ba a gini sai da ginshiki, Malamin sai ya da ya fara da bayyana su waye Yahudawa, asalinsu, ta'asarsu, matsayinsu a wajen musulmi, matsayin kiristoci a wajensu, manufarsu ga duniya da kuma yadda suke kallon duk wani mutum da ba Bayahude ba.
Duk da yake cewa bai samu isasshen lokacin da zai warware zare da abawa ba, amma Shehin Malamin ya zungoro kusan duk wani makirci na Yahudawa tun a zamanin Annabi Musa zuwa yanzu. Ya kwance masu zani a kasuwa fiye da kowane lokaci. Ya ce a wajensu duk wani wanda ba Bayahude ba shi bawan Yahudawa ne. "Babbar manufar Yahudawa ita ce su mallake duniya."
Shaikh Dakta Yusuf Ali ya tabbatar da cewa a cikin Alkur'ani Allah ya bayyana hakikanin Yahudawa da kuma irin ta'asar da suka yi na kashe Annabawa da kuma jefan mutane kwarai da miyagun kalamai. Ya ce suna danganta kansu da Annabi Ibrahim da kuma Annabi Yakub da Musa. Ya hakaito irin yabo da zargin da Alkur'ani ya yi wa Yahudawa. Ya ce an samu kalmar Yahudu ne daga Yahuza dan Annabi Yakuba na hudu.
Za mu ci gaba insha Allah.

  | 


TV dinner still cooling?
Check out "Tonight's Picks" on Yahoo! TV.

__._,_.___
Recent Activity
Visit Your Group
Yahoo! Avatars

Share Your Style

Show your face in

Messenger & more.

Yahoo! Mail

Get on board

You're invited to try

the all-new Mail Beta.

Y! Messenger

Quick file sharing

Send up to 1GB of

files in an IM.

.

__,_._,___

No comments: