Index

Tuesday, April 10, 2007

[kanoshia] JAWABIN MALAM ZAKZAKY (H) NA RANAR MAULUD A ZARIYA

BUKIN MAULUDIN MANZO (S) NA ZARIYA YA KAYATAR
 Daga: Muhammad Mansur
Kamar yanda aka saba a kowane wata na Rabiul Awwal din kowace shekara, harkar musulunci karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) tana gabatar da taron makon hadin kai tun daga ranar 12 ga watan har zuwa 17 ga watan inda Malam din ne da kansa kan gabatar da jawabin rufewa bayan kammala muzaharar da 'yan'uwa kan gabatar don murnar wannan rana. A bana ma kamar kullum, ranar Alhamis 17 ga Watan na Rabiul Awwal 1428 wanda ya yi dai dai da 5 ga Maris 2007 dubun dubatan 'yan'uwa musulmai ne daga garuruwa daban-daban na fadin Najeriya da makwabtanta suka taru a birnin Zariya domin halartan shagulgulan bukin mauludin Manzon Allah (s.a.w.a) wanda harka kan shirya a duk shekara.
Taron na bana ya samu mahalarta daga garuruwa daban-daban ciki kuwa har da  maza, mata, yara da tsofaffi kamar dai kullum. Tun da misalin karfe bakwai ne na ranar 'yan'uwa suka fara tururuwa zuwa birnin na Zariya inda suka shiga sahun muzaharar da ake gabatarwa don murnar wannan rana mai albarka. Muzaharar dai an kasata biyu ne domin yawan mahalartan. A yayin da garuruwan da suka fito daga hanyar Kano, Katsina, Sokoto, Zariya dss suka taso daga masallacin Sabon gari, garuruwan Kaduna, Patiskum, Lagos, Abuja, dss suka dauko sahun muzaharar daga Gwargwaje.
Mahalarta muzaharar suna tafe cikin ado, annashuwa da murna suna tafe suna wakokin Manzon Allah da Iyalansa (AS) suna kuma raba kyaututtuka ga jama'ar Annabi da suka fito gefen titi suna kallon muzaharar.
An dai kammala muzaharar ne a filin kwallon kofar doka inda aka taru domin sauraron jawabi daga bakin Malam Ibraheem Zakzaky (H).
Malam (H) ya fara jawabi ne da yiwa Allah godiya, ya kuma ci gaba da kawo muhimmancin wannan rana tare da albarkokin da ke cikin ta na haihuwar Manzon Allah (S.A.W.A.). Malam ya ci gaba da kawo irin abubuwan da suka faru na mu'ujizojin a irin wannan rana da aka haifi fiyayyen talikai don busharar da zuwansa. Wannan kuwa ya hada da rushewar katangar Kisra (Caesar) tare da bayyanar haske a duk fadin duniya. Haka kuma Malam yace Manzon Allah Ya sha wahala wajan isar da sako inda ya kawo yanda Manzo duk da irin munanan halayen da al'umma ta kasance amma sai da ya shiryar da ita al'umma din. Duk da kuwa ya samu larabawa cikin wani yanayi na kabilanci da gaba ta yanda kowa yana jin zai iya kashe kowanene akan jinnin dan uwansa, har ma ta kai ga mutane suna kwana ne da takubbansu. Amma sakamakon bayyanar wannan haske sai gashi al'umma ta gyaru.
A cikin jawabin nasa Malam ya nuna takaicinsa ta yanda a yau musulmi bashi da wani kima a idon duniya, shine abin kashewa, a kowace kusurwa ta duniya. Ana kashe musulmai a kwace masu dukiyoyi da sunan yaki da ta'addanci. Malam ya kara da cewa abin bakin ciki shine ta yanda wannan cin mutuncin har yakai ga ana taba martabar Manzon Allah da sunan yaki da ta'addanci. Ya nusar da cewa ba komi ya sanya makiya musulunci suka tashi suna yakar addini ba sai don ganin addini yana yunkurowa. Addini ya farfado ya bunkasa a sassa daban-daban na duniya, yace wannan ne ya basu tsoro shi yasa suka tashi haikan suna yakar addini.
A karshen jawabain na Malam (H) ya kuma ja kunne ga al'ummar musulmai da cewa wannan zabe da ake ta kururuwarsa a Najeriya ba komi bane illa yaudara, haka kuma ya ankarar da halin wahalar da ake ciki a kasar ta yanda hatta a sibitoci suka zama makasa mai makon wurin jinya saboda rashin kayan aiki. Malam yace siyasa ba itace mafitar al'umma ba. Mafita daya ce shine bore ga azzalumai da nufin tabbatar da addinin Allah. Ya kuma nuna damuwarsa tare da yin Allah-wadai ga azzaluman kasa da ke ta hankoron azabtar da al'umma tare da kada jama'a kamar shanu.
Malam ne dai ya rufe taron da addu'a inda yayi fatar Allah Ya tabbatar mana da addini Ya tseratar da al'umma daga zalunci. 
 


Now that's room service! Choose from over 150,000 hotels
in 45,000 destinations on Yahoo! Travel
to find your fit.

__._,_.___
Recent Activity
Visit Your Group
Yahoo! Avatars

Make a Virtual You

Show your style &

mood in Messenger.

Y! Messenger

Group get-together

Host a free online

conference on IM.

Yahoo! Mail

Next gen email?

Try the all-new

Yahoo! Mail Beta.

.

__,_._,___

No comments: